Ba za a yi sanyin hunturu a bana ba – Masani

Wani masani yanayi a Najeriya Hussaini Jarkasa, ya bayyana cewar a bana ba za a samu yanayin sanyi ba kamar yadda aka saba gani a shekarun baya ba.

Masanin ya bayyana cewar a bana an samu gagarumin Sauyin da ba za a samu sanyin hunturu a bana ba yadda aka saba, a cewar sa hakan ya faru ne sakamakon sare dazuka da ake yi ana kone bishiyu domin yin gawayi ko itace domin yin girki.

Masanin Malam Hussaini Jarkasa. Ya kara da cewar sakamakon yawan sassare bishiyoyi da kuma kone daji da kuma hayaki ya sanya aka samu sauyin yanayin da ba za ayi sanyi hunturu mai karfi ba a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here