Advert
Home Sashen Hausa Ba ni na sace kuɗin gasar rubutu ta Katsina ba, inji Shehu...

Ba ni na sace kuɗin gasar rubutu ta Katsina ba, inji Shehu Gombe

Ba ni na sace kuɗin gasar rubutu ta Katsina ba, inji Shehu Gombe

MUTUMIN da ake zargi da yin awon gaba da zunzurutun kuɗi har N250,000 na ladar lashe wata gasar rubutu da aka yi bikin ta a Katsina jiya ya musanta zargin da ake yi masa.

Wani babban ɗan siyasa kuma ɗan kwangila mai suna Architect Ahmed Musa Ɗangiwa, wanda shi ne Manajan Darakta na Bankin Bada Lamunin Mallakar Gidaje na Tarayya (wato Federal Mortage Bank of Nigeria, FMBN), shi ne ya ɗauki nauyin gasar a ƙarƙashin sabuwar Gidauniyar Haɓaka Adabi ta Architect Ahmed Musa Ɗangiwa.

Taken ta shi ne “Rubutun Hausa a kan Muhalli” kuma wannan shi ne karo na farko da aka shirya ta.

Bilkisu Muhammad Garkuwa ita ce ta zo ta biyu

Labari ya ɓulla jim kaɗan bayan an tashi daga taron cewa an sace wa wanda ya zo na ɗaya a gasar, wato Malam Bishir Adam, kuɗin ladar sa ta cin gasar. An zargi wani marubuci mai suna Malam Shehu T. Abdullahi Gombe, wanda ya halarci bikin bada kyaututtukan daga garin Gombe, da laifin sace kuɗin.

Shehu ma ya shiga gasar amma Allah bai ba shi ikon ci ba.

Bishir, wanda ya zo na ɗaya, ya faɗa wa mujallar Fim cewa ya bada kuɗin ne ga mutumin lokacin da su ke zaune tare, ya ce ya riƙe masa saboda za su yi hoto da Architect Ɗangiwa da sauran zakarun gasar da masu shirya gasar.

Da aka gama ɗaukar hoton, ya faɗa wa Shehu an yi masa sata, shi kuma ya ce bai ɗauka ba.

Aliyu Rabe Aliyu, na uku a zakarun gasar

Kuɗin dai su na cikin wani babban ambulan ne tare da jakar kwali da aka raba a taron. A ciki akwai kuma kyautar wata ƙaramar waya da aka ba shi da hatimin cin gasar.

Sace kuɗin ya haifar da muhawara mai zafi a ƙarshen taron, kuma abin ya ba kowa mamaki da takaici.

Sai dai Malam Shehu ya tabbatar wa da mujallar Fim a hirar da ya yi da ita a daren jiya a Katsina cewa shi kam bai ɗauki kuɗi ba.

A cewar sa, shi marubuci ne wanda ya zo taron daga Gombe, kuma sun haɗu da Bishir ne a wurin taron.

Teburin manyan baƙi lokacin da ake buga taken Nijeriya

Ya ce: “Mun yi sallah tare, har ma mu ka shigo mu ka zauna wuri ɗaya mu na ta taɗi. To mu na taɗi har ya je ya karɓo kyautar da ya zo na ɗaya ya dawo, ya zo da kayan, mu ka shirya mu ka saka a cikin jakar; waya aka ba shi da wani kwali, ya saka a ciki.

“Lokacin da ya saka a ciki, sai aka nemi za su ɗau hoto. Sai ya ba ni ajiyar kwalin na riƙe. To riƙewar da na yi, sai kuma wataƙila ya na da buƙatar su, sai ya taso zai karɓa. Sai na ɗau tashi sai na miƙa masa.

“To, ni waya ta mu na ɗaukar hoto sai ta faɗi ta fashe. To gaba ɗaya sai jiki na ya mutu saboda ba ni da ‘communication’, sai na zauna, na rasa yadda zan yi saboda ban da wata waya, ita kaɗai ce.

“Akwai wani wanda ake ce masa Majiya wanda a hannun sa wayar ta fashe, sai ya zo ya ce, ‘Fito, fito!’

“Mun fita waje sai na gamu da shi kuma (Bishir) ya na taɗi. Ya kira ni gefe ya ce min kuɗin nan fa da aka ba shi a cikin enbelof an ɗauke. Sai na ce, ‘An ɗauke, kamar ya?’

“Sai ya ce da man ya na cikin wannan kwalin da ya saka. Sai na ce, ‘To?! Wallahi ban gani ba’.

“Ya ce min na gani? Na ce wallahi ban gani ba.

“Mu ka yi abu kamar wasa fa, ya na gaya min, na ce na dai ga kwali da sauran abubuwan da aka saka a ciki, amma ban ga wannan enbelof da ya ke magana ba.

“Sai yanzu kuma an zo nan, shuwagabannin taro su ka zo su na tambaya ta, na gaya masu abin da ya faru daga farko har ya zuwa yanzu.

“Kuma sun je ɗaki na, sun bincika, ba su ga komai ba. Shi ne kawai abin da na sani.”

Ɗaya daga cikin masu shirya gasar, Malam Yazid Nasudan, ya faɗa wa mujallar Fim cewa za su zauna da Bishir domin samun cikakken bayani kan yadda al’amarin ya faru.

A cewar sa, da farko sun so su yi diraf na kuɗin, maimakon a je wurin taron da tsabar su, to amma wasu ‘yan kwamitin shirya gasar su ka ce gara a ba kowa kuɗin sa a hannu a wajen taron.

In da an yi diraf an ba kowa, to da satar ta zama a banza domin ɓarawon da ya yi satar ba zai iya karɓar kuɗin a banki ba.

Da wakilin mu ya tambayi Nasudan ko akwai yiwuwar ba Bishir ɗan wani hasafi saboda asarar da ya yi, sai ya ce za su sanar da Ɗangiwa abin da ya faru kafin a yanke shawara a kan hakan.

Shi ma Bishir ya shaida wa mujallar Fim cewa da gaske an yi satar.

Ya ce babu shakka ya san wanda ya ba ajiyar kuɗin, kuma ya dai zura ido ne ya ga yadda lamarin zai wanye.

Bai daɗe da faɗin haka ga mujallar Fim ba sai Bashir ya kira wa Shehu ‘yansanda domin su yi bincike, inda su ka tasa ƙeyar sa zuwa ofishin su. A can ya kwana.

Bishir ya ce wasu ‘yan’uwan sa ne su ka ba shi shawarar ya yi ƙarar Shehu wajen ‘yansanda.

Wata majiya ta shaida wa wakilin mu cewa an yi da Bishir cewa zai je ofishin ‘yansandan kafin ƙarfe 10 na safiyar yau, kuma idan bai haƙura da kes ɗin ba to za a kai su kotu shi da Shehu kamar yadda doka ta tanada.

Sai dai mujallar Fim ta gano cewa tun a jiya masu shirya taron tare da sauran marubuta su ka yanke shawarar yin karo-karo na kuɗi domin a ba Bishir saboda asarar da ya yi.

Majiyar ta ce an yi haka ne domin da yawa sun yarda da cewa alamu da dama sun nuna cewar ba Shehu ba ne ya sace kuɗin.

Saboda haka, an yanke cewar duk abin da zakarun gasar su ka tara ta hanyar tarbace, su mashirya gasar za su cika su ba Bishir “ko da N100,000 ne”.

Tuni dai wadda ta zo ta biyu a gasar ta bada gudunmawar N10,000, sauran kuma sun fara bayar da N5,000 kowannen su.

Majiyar ta ce zuwa yanzu an tara abin da ya haura N50,000.

Shi dai zakaran gasar, wato Malam Bishir Adam, ɗan Katsina ne. Wadda ta zo ta biyu a gasar, Bilkisu Muhammad Garkuwa, ‘yar Kano ce, sai kuma na uku, Aliyu Rabe Aliyu, shi ma ɗan Jihar Katsina ne wanda ke zaune a Abuja.

Mutum 18 ne dai su ka lashe gasar, sannan akwai mutum 17 da su ka shiga gasar amma ba su ci ba.

An ba wadda ta zo ta biyu tukwicin N150,000, na uku kuma tukwicin N100,000. An ba kowannen su kyautar ƙaramar waya da littafin labaran da su ka shiga gasar.

Daga kan na 4 zuwa na 13 kuma an ba kowa N50 da kyautar ƙaramar waya da littafin labaran.

Su ma sauran mutum 17 da ba su ci gasar ba, an ba kowannen su N15,000 da kyautar waya.Wadda ta zo ta biyu a gasar, Bilkisu Muhammad Garkuwa, ta shaida wa mujallar Fim cewa farin cikin ta ba zai misaltu ba saboda wannan nasara da ta samu.

Ta yi godiya ga Allah da ya kawo ta wannan matsayi, kuma ta gode wa masu shirya gasar.

Ta ce ga shi dai ita ba ta san kowa a cikin masu shirya gasar ba, amma ta shigar da labarin ta, kuma Allah ya sa ta zo ta biyu.

Bilkisu, wadda ta ce wannan shi ne karo na farko da ta shiga wata gasar rubutu, ta yi kira ga marubuta da su ɗauki harkar rubutu da muhimmanci, su dage sosai wajen yin rubutun.

Ita ce dai marubuciyar littafin ‘Ita Ce Zaɓi Na’ wanda aka wallafa shekara biyar da su ka gabata.

An yi jawabai a taron, ciki har da na Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, wanda ya jinjina wa mashirya taron, musamman Architect Ɗangiwa da ya ɗauki nauyin shirya gasar.

Gwamnan ya yi kira a kan sauran hukumomi da su tashi su riƙa shirya gasa irin wannan don alkinta harkar adabin Hausa.

Haka kuma ya yi kira ga marubutan Hausa da su dage, sannan kuma ya yi jinjina a gare su.

Masari ya sha alwashin cewa gwamnatin sa za ta amsa kiran da aka yi mata na ƙarfafa harkar rubutu a jihar.

Tun da fari sai da ɗaya daga cikin manyan baƙi a taron, Farfesa Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ya yi jawabi inda ya bada tarihin shirya gasar rubutu wanda ya samo asali a Katsina tun daga zamanin mulkin Turawa.

Ya yi nuni da cewa Katsina ƙasa ce mai cike da ‘yan boko da malamai da marubuta tun daga zamanin dauri har ya zuwa yau.

Malumfashi ya yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta ci gaba da ƙarfafa wa marubutan Katsina gwiwa ta hanyar shirya gasar rubutu irin wannan.

Mahalarta taron

Haka kuma ya yaba wa Ɗangiwa saboda ƙwazon da ya nuna wajen ɗaukar nauyin wannan gasar. Ya ce ya kamata a maida wannan gasa ta Ɗangiwa zuwa ta shekara-shekara.

Tun da farko, a nasa jawabin, Architect Musa Ɗangiwa ya bada labarin yadda aka assasa wannan gasa da ya ɗauki nauyin shiryawa.

Ya ce da fari ma bai ɗauki abin da gaske ba lokacin da masu shirya gasar su ka same shi da maganar, amma daga baya ya ga cewa lallai babban al’amari ne, kuma ya maida hankalin sa a kai.

Ɗangiwa, wanda  ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Kankiya ta Jihar Katsina ne, ya ce ya yi murnar ganin yadda abin ya kasance.

A taron dai an ƙaddamar da littafin, inda mutane da dama su ka faɗi abin da za su bayar na gudunmawa.

Wani sashe na mahalarta taron

Taron ya yi armashi kuma ya samu halartar ɗimbin jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Waɗanda su ka halarta sun haɗa da manyan ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, malaman jami’a, marubuta da kuma ‘yan kasuwa.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Har yanzu: Gwamna Masari na Alhinin Rasuwars Kwamishinan Kimiyya Rabe Nasir

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa...

Katsina lawyer in court over alleged cheating,forgery, impersonation

A Funtua based Company in Katsina state, NAK International Merchant has dragged a Lawyer, Barrister Mahdi Sa'idu to court over alleged cheating, forgery and...

The YOUTHS ASK YAHAYA BELLO FOR PRESIDENT MOVEMENT (YAYBP) under the Leadership of their Founder/National Coordinator Alhaji Ibrahim Muhammad on Saturday 15th January, 2022...

The movement, which said the gesture is part of its efforts to alleviate the sufferings of the less privileged in the society through its...

Bin Sa’id Tsangaya Model School Ta Yi Bikin Saukar Dalibai.

Daga Auwal Isah. A karon farko, Makarantar hardar Alkur'ani mai tsarki ta " Bin sa'id Tsangaya Model School " da ke a unguwar Tudun 'yan...

Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Kwamishina Rabe Nasir A Jihar Katsina

Ziyarar Da Jigon Jam'iyyar APC Na Kasa, Tsohan Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo A Jihar Katsina, Domin Yin Ta'aziyyar Rasuwar...