Ba Ni Na Fara Fadin Maganar Al’umma Su Kare Kansu Ba, Cewar Gwamna Masari

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi watsi da kiran Gamayyar Kungiyoyin arewa (CNG) na yayi murabus saboda ya ce mutane su kare kansu daga yan bindiga.

Masari ya ce ba shine gwamnan farko da ya faɗawa mutane su kare kansu daga ta’addancin yan bindiga ba, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Gwamnan ya kara da cewa kiran da ake masa ya yi murabus daga kujerarsa wata alama ce ta rashin fahimtar halin da kasar nan take ciki.

Jihar Katsina na fama da hare-haren yan bindiga, inda suke sace mutane domin neman kuɗin fansa da kuma kashe su ba gaira babu dalili.

Da yake jawabi a wata ziyara da ya kai Jibiya, Gwamna Masari ya bukaci mutanen jihar Katsina su tashi tsaye su kare kansu daga yan bindiga.

A wani jawabi da shugaban ƙungiyar CNG reshen yankin arewa maso yamma, Jamilu Charanci, ya fitar, ya ce kiran da gwamnan ya yi na mutane su kare kansu ya nuna cewa ba shi ke da akalar juya jihar ba.

Charanchi ya kara da cewa saboda haka gwamnan ya gaza sauke nauyin da aka ɗora masa na samar da tsaro, don haka ya yi murabus.

Da yake martani a wani jawabi da kakakinsa, Abdul Labaran, ya fitar, Masari yace wata barazanar tsirarun mutane dake ikirarin kare hakkin dan adam ba zata sanya ya yi murabus ba.

Audu Labaran ya ci gaba da cewa “A lamarin tsaro, gwamna shine shugaban jami’an tsaro a jiharsa, amma a suna ne kawai saboda shugabannin hukumomin tsaro ba daga hannun gwamna suke karbar umarni ba, daga manyan su na Abuja ne.”

“Masari ba shine gwamna na farko da ya fara wannan maganar ba. Duk jihar da mutanenta ba su saka siyasa a lamarin tsaron su ba, za ka samu shugabannin su suna kara musu karfin guiwa.”

“Duk wanda yake ganin Masari ya yi murabus kan baiwa jama’ar da yake jagoranta muhimmanci da kara musu karfin guiwar su kare kansu, to sam bai ma fahimci sakon ba da kuma kundin tsarin mulki ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here