Ba na tsoron kowanene shugaba a 2023 – Buhari

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce shi bai damu da wanda zai gaje shi ba a matsayin shugaban a shekarar 2023.

Buhari ya tabbatar da hakan ne a hirarsa da kafar talabijin ta Channels TV a yammacin Laraba.

Ya bayyana cewa “Zaɓen 2023 ba matsalata ba ce”.

“Ban damu da wanda zai gaje ni ba, rabu da shi ya zo ko ma wane ne,” in ji shi.

Da ya ke amsa tambaya kan ko me ke zuwa masa a rai idan ya ji an ambaci zaɓen 2023, Buhari ya amsa da cewa: “Ba matsalata ba ce.”

Da aka tambaye shi: “Ba ka damu game da wanda zai gaje ka ba? Sai ya ce:

“Bar shi ya zo ko ma wane ne. Na tabbata na ajiye rahoton duk wani abu mai muhimmanci. Bai kamata wani ya kira ni ba da shaida a gaban kotu ba a kan wani abu, idan ba haka ba kuma zai shiga matsala.”

Buhari ya ce duk da cewa ba shi da wani ɗan takara da ya ke goyon baya a jam’iyyarsu ta APC mai mulki ya gaje shi, amma idan ya bayyana shi za a iya halaka shi.

“A’a, saboda idan na faɗa za a iya kawar da shi. Gara na bar shi a sirrance,” A cewar Buhari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here