Advert
Home Sashen Hausa Ba Na Hanzarin Yin Takarar Shugaban Kasa A 2023 — Kwankwaso

Ba Na Hanzarin Yin Takarar Shugaban Kasa A 2023 — Kwankwaso

Ba Na Hanzarin Yin Takarar Shugaban Kasa A 2023 — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu bai yanke shawawar tsayawa takarar shugaban kasa ba a babban zabe mai zuwa a shekarar 2023.

Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na DW a ranar Laraba, inda ya ce yana tattaunawa tare da tuntubar masu ruwa da tsaki don yanke hukuncin da ya dace.

Ya ce, “A wannan lokaci ba hanzari muke yi ba, don haka muna bibiyar komai a sannu, sannan muna neman shawarar wadanda suka dace kuma za mu yanke hukunci kuma mu sanar da mutanenmu.

“Muna da tarin magoya baya da suka isa mu yi kowace takara. Muna da mutane a ko’ina a Najeriya. Wasu na tunanin a Kano ko Arewa muke da magoya baya, amma ba haka abun yake ba, don muna da magoya baya a yankin Asiya, Amurka har da nahiyar Turai,” cewar Kwankwaso.

Kazalika, ya musanta rade-radin da ake na cewa shi da magoya bayansa na shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, inda ya ce babu wani abu mai kama da hakan.

“Batun sauya shekata zuwa APC an dade ana yin sa a lokuta mabambanta. Wannan ba shi ne karo na farko da hakan ta taba faruwa ba. Mutane da dama suna ta magana a kai, don dole ya zama abun farin ciki a ce kowa na magana a kanka. Wannan na nuna nagarta da jajircewar da muke da ita.

“A yanzu ba ni da masaniya a kan hakan kuma ban shiga tattaunawa da kowa ba don komawa APC. Wannan shi ne abin da zan iya cewa a yanzu,” kamar yadda ya bayyana.

Tsohon Sanatan ya ce siyasa na son yin aiki tukuru da jajircewa, wanda hakan zai sa mutum ya samu gogewa.

Source: Aminiya

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

10 ROAD REHABILITATION PROJECTS COMPLETED IN KEBBI STATE!

#PositiveFactsNG Do you know that the Buhari administration has just concluded the rehabilitation of 10 roads in Kebbi State under the Special Maintenance, Repairs and...

Ba abinda zai dawo da ni harkar siyasa — Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo a ranar Asabar ya sake jaddada ƙudurinsa na ficewa daga harkokin siyasa, inda ya ce babu abin da zai...

CONSTRUCTION OF THE BARO – MINNA RAIL LINE IS SET TO COMMENCE!

#PositiveFactsNG To maximise the business opportunities that the Baro Seaport will unleash when completed, do you know that the Buhari administration has recently awarded the...

Al’uma ciki da wajen Najeriya suna tururuwa zuwa ta’aziyyar rasuwar Mahaifiyar Alhaji Ɗahiru Mangal: Tsohon Shugaban ƙasar Nijar, da Gwamnan Kano sun sun isa...

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci tawagar Gwamnati zuwa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Dahiru mangal...

ZUWAN DALLAZAWA SAFANA, DA ASALIN GIDAN YARIMA DAKE CIKIN BIRNI KATSINA.

Dallazawa sune zuri'ar Malam Ummarun Dallaje. Ummarun Dallaje kamar yadda Tarihi ya nuna shine Sarkin Katsina na farko daga tsatson FULANI, Kuma daga cikin...