Advert
Home Sashen Hausa Ba mu karbi ko sisi ba, amma mun karbi kayan abinci." Inji...

Ba mu karbi ko sisi ba, amma mun karbi kayan abinci.” Inji Minista Sadiya.

Ministan jinƙai Hajiya Sa’adiyya Umar Farooq

Ba mu karbi gudummawar kudin korona ko ta sisi ba -Minista Sadiya

Ministar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ta ce ma’aikatar ta ba ta amshi gudummawa ko ta sisi, a nan cikin gida da kuma kasashen waje, da sunan tallafin korana ba.

Sadiya ta bayyana haka a lokacin da ta ke kare kasafin ma’aikatar ta na 2021, a gaban kwamitin Majalisar Tarayya.

Ministar ta yi wannan ikirari bayan Najeriya ta karbi bilyoyin kudade a matsayin kudaden gudummawar tallafi da yaki da cutar korona, daga hannun kamfanoni, bankuna da daidaikun jama’a.

Sadiya ta ce ko sisi ba a bai wa ma’aikatar ta ba a cikin kudaden wadanda wasu daidaikun jama’a da kamfanoni su ka bayar gudummawa.

Ya zuwa karshen watan Afrilu, kudaden da Najeriya ta tara daga gudummawa, sun kai naira bilyan 27.160.

Ta ce amma ba a bai wa ma’aikatar ta ko sisi ba.

Wasu da su ka bada gudummawa mai tsoka sun hada da Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu, Segun Agbaje (GTB), Tony Elumelu (UBA), Oba Otudeko (First Bank), Jim Ovia (Zenith Bank), Herbert Wigwe (Access Bank) da kuma Femi Otedola (APD).

Da ta ke magana a kan rabon tallafi, cewa ta yi ma’aikatar ta abinci kawai ta karba daga hannun gwamnatin tarayya.

Ba mu karbi ko sisi ba, amma mun karbi kayan abinci.” Inji Minista Sadiya.

Ta kara da cewa baya ga kasafin ma’aikatar, ba su karbi karin kudi ko naira daya daga hannun gwamnatin tarayya da sunan kudaden tallafin raba wa jama’a ba.

Sadiya ta kara da cewa daga cikin kasafin ma’aikatar, kashi 50 kadai ta iya karba daga hannun gwamnatin tarayya.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

MATSALAR TSARO: Yanda Al’umar garin Mada, dake ƙaramar Hukumar mulkin Gusau suke barin gidajen su…

Matsalar Tsaro: Yadda al'umar garin Mada dake karamar hukumar mulkin Gusau ta jihar Zamfara ke barin matsugunnansu a safiyar yau Asabar sakamakon ta'azarar hare-haren...

An Kwakule Idon Wani Karamin Yaro A Bauchi

An Kwakule Idon Wani Karamin Yaro A Bauchi  -Aminiya- An kwakule idon wani karamin yaro mai shekara 16 a Kwanan Gulmanmu da ke Unguwar Jahun...

Hajj 2022: Dalilin Rashin Tashin Maniyyata Daga Filin Jirgin Jos

Hajj 2022: Dalilin Rashin Tashin Maniyyata Daga Filin Jirgin Jos Maniyyata aikin Hajjin bana daga Jihar Filato ba za su samu tashi daga Babban Filin...

PHOTOS: Kwankwaso, Fayose Visit Wike

The presidential candidate of the New Nigeria People’s Party, Rabiu Kwankwaso, on Friday visited the Rivers State Governor, Nyesom Wike in Port Harcourt. Also present...
%d bloggers like this: