Home Sashen Hausa Ba a saka ranar naɗa sabon Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya...

Ba a saka ranar naɗa sabon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Ba a saka ranar naɗa sabon Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Garba Shehu

Fadar Shugaban Najeriya ta ce ba a saka wata rana ba domin sanar da sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan ƙasar yayin da wa’adin babban sufeton yake ƙarewa a yau Litinin.

A yau Litinin Mohammed Adamu yake cika shekara 35 da fara aikin ɗan sanda, bayan ya shiga aikin ranar 2 ga watan Fabarairun 1986.

Sai dai mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya faɗa a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a safiyar yau cewa ba shi da wata masaniyar ranar da za a bayyana sabon shugaban ‘yan sandan.

“Shugaban ƙasa zai koma Abuja ranar Talata, ” a cewarsa. “Zai shiga ofis zuwa Laraba. Ban san lokcin da zai yi hakan ba. Amma abin da zan tabbatar muku shi ne, manyan muƙamai irin wannan ba a barinsu haka, saboda haka tsarin zai tsaftace kansa,” in ji Garba Shehu.

Kazalika, Garba ya ce naɗin sabon sufeto janar ɗin zai kasance bisa cancanta ba tare da duba ƙabila ba.

“Shugaban ƙasa zai so ya naɗa sufeto janar da zai kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba wanda ‘yan ƙabilarsa ke yabonsa ba,” a cewarsa.

An naɗa Mohammed Adamu a matsayin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya a watan Janairun 2019 kuma zai cika shekara 60 da haihuwa ranar 17 ga watan Satumba.

Kazalika, loƙacin ritaya na wasu manyan jami’an ‘yan sanda 13 ya yi, waɗanda suka haɗa da DIG guda uku da kuma AIG guda 10.

Sai dai Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa Shugaba Buhari damar tsawaita zaman sufeto janar na ‘yan sandan idan yana da niyyar yin hakan.

Wasu jaridu a Najeriya sun ruwaito cewa Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Mohammed Maigari Dingyadi ya gabatar wa Buhari jerin sunayen wasu mataimakan sufeto janar (DIG) domin zaɓar sabon sufeton daga cikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: