Mu’azu Hassan @katsina city news
Wani binciken da jaridun katsina city news su kayi, akan wadatuwar man fetur dai dai gwargwado a birnin katsina shine yadda gidaje man Dan marna, suka rike wuta wajen sauke Man fetur kusan kullum a daya ko biyu ko uku na gidajen man da suke sayar da mai.
Mun gano yayin da wasu gidajen Man, sun sauke kadan, daga kwanaki kadan kafin fara azumi zuwa yau talatin da wata na Ramadan .
Gidajen Man Dan marna kusan kullum akwai inda ake bayar da Man fetur.
Wannan kokarin na gidajen Man Dan marna ya Sanya sauran gidajen man masu samo mai ta bayan fage suna tsawalla kudi dole suka rage farashin.
Wannan kokarin na gidajen man Dan marna a wannan wata mai Albarka abin a yaba ne.
Hatta yau talatin ga watan Ramadan gidajen mai uku na Dan marna ke bayar da mai a garin katsina. Kamar yadda muka gani.
Sune kofar Durbi.kofar kwaya hanyar Dutsinma da kuma kuma Barhim.
Wannan ya karya wahalar fetur da akan shiga a daren sallah, ta fada har bukukuwan sallah
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779