Home Sashen Hausa Ayyukan Ta’adanci: Ƴan Bindiga Sun Hana Ƴan Kasuwa Komawa Garuruwan su a...

Ayyukan Ta’adanci: Ƴan Bindiga Sun Hana Ƴan Kasuwa Komawa Garuruwan su a Jihar Katsina.

Ayyukan Ta’adanci: Ƴan Bindiga Sun Hana Ƴan Kasuwa Komawa Garuruwan su a Jihar Katsina.

Wasu gungun ‘yannkasuwa a saman hanya zaune suna fargabar barayi sun tare su

 

 

A jiya Talata 18/05/2021 ƴan Bindiga sun hana daruruwan ƴan kasuwa komawa gidajensu bayan sun kammala hidindimun cin Kasuwar garin Ƙanƙara.

Ƴan ta’addar dauke da bindigu sun tare hanyar data tashi daga garin Ƙanƙara Zuwa Kaikabayas, Malali, Pauwa, Zangon Zabaro, Makera, Dansabau har zuwa garin hayin Bedi dake cikin Jihar Zamfara da misalin karfe 4:30.

Majiyar mu ta tabbatar mana cewa har zuwa daren ƴan kasuwar na jibge agefen hanyar dake bakin garin na Ƙanƙara, suna jiran gawon shanu.

A zantawar da Wakilin Rana24 yayi da wasu daga cikin ƴan Kasuwar da aka tare hanyar tasu ya bayyana cewa sun tsayane domin labarin da suka samu cewar ‘ƴan ta’adda ne suka tare hanyar komawarsu gidajensu.

Hakazalika wani direba ya kara dacewa bayan ya kammala lodi ne yakama hanyarshine ta komawa gida yayi cinkaro da shugaban tsaro na Ƙaramar hukumar Ƙanƙara wato DPO cikin mota maisulke inda ya umurceshi daya dawo Hanyar bata da kyau inda nan take ya juya da motar shi zuwa dawowa cikin garin Ƙanƙara domin tsira da rayuwakansu.

Direban yakuma koka da irin tsananin Matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin nasu, Bugu da Kari ‘ƴan Bindiga sun sha alwashin hana Noma awannan yanki daya shafi Kankara da wasu yankunan Faskari, Hayin Bedi, dake cikin Jihar Zamfara.

Daga Karshe al’ummar wannan yankin sunyi kira ga Gwamnatin data sanarda da isassun Jami’an tsaro da kuma Samar masu isassun Kayayyakin aiki da Kuma basu damar yin aikin tsaro.

Kazalika dai ko a Jiyan Barayin ɗauke da muggan Makamai ne suka dira a Batsari inda sukai harbin kan mai Uwa da Wabi, kawo yanzu baa samu rahotannin rasa Rayuka ba saboda Jami’an tsaro da suka far masu.

Haka Lamarin yake a ƙaramar hukumar Safana Inda Barayin sukayi awon gaba da wani Alƙali na kotun Shari’ar Musulunci mai Suna Hussaini Samaila.

Allah ya kyauta ya kawo mana ƙarshen wannan Ibtila’in Amin.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here