Shugaban Karamar Hukumar Birni da Kewaye, Ya fara aikin kafa kofofi 20 masu karfin gasken da zasu zagaye wasu unguwanni 6, ciki harda da wani bari a karamar hukumar Gwale.

Mai girma zababben Chairman Kano Municipal Hon. Faizu Alfindiki, ya amince da girka kofofi don magance kalubalen tsaro a sassa daban-daban na birni a kokarin sa na Inganta harkar tsaro.

Daga cikin wuraren da aka amince da wadannan kofofin akwai:

1) Marmara

2) Akwa

3) Alfindiki

4) Kududdufawa

5) Mazan Kwarai

6) Kwanar Goda

Wadannan su ne wuraren da za’a fara kafa kofofin, ayayin da za’a sanya guda 20 cikin lungunan unguwannin, kuma za a rufe su da zarar dare ya yi sannan za a baza jami’an tsaro na musamman a kowace kofa don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zukatan mutanen Birni da Kewayen Birni.

Office of the Executive Chairman Kano Municipal Local Government Council.
Today Thursday, 8th March 2021.
#Faizualfindiki #FASM #RealUYusuf

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here