Ayatollah Khamenei ya yi wa Trump barazana kan kisan Soleimani

Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Twitter mai kama da barazanar kai hari ga tsohon Shugaban Amurka Donald Trump domin ramuwar gayya kan kisan babban kwamandan ƙasar da Amurka ta yi a bara.

Saƙon da Ayatollah ya wallafa ya nuna wani mutum mai kama da Donald Trump tsaye yana buga wasan lambu, kuma an ɗauki hoton kamar daga saman jirgi ko kuma amfani da jirgi mara matuƙi.

A saƙon, ya ce “ramuwa ba makawa”.

Tuni dai wasu masu amfani da shafin Twitter suka fara kira da a dakatar da shafin shugaban addinin.

A yanzu dai shafin na Twitter ya dakatar ɗaya daga cikin shafukan Ayatollah (@Khamenei_Site) kamar yadda aka dakatar da na Trump a kwanakin baya sakamakon ya wallafa wasu saƙonni da suka saɓa ƙa’ida.

A bara ne dai wani jirgi mara matuƙi mallakar Amurka ya kai hari ga Janar Qasem Soleimani inda ya kashe shi a Bagadaza.

Sai dai a lokacin, Mista Trump bai nuna nadama kan haka ba inda ya ce Qasem Soleimani ya yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here