Advert
Home Sashen Hausa Atiku ya zargi Buhari da karya masa harkokin kasuwanci

Atiku ya zargi Buhari da karya masa harkokin kasuwanci

Atiku ya zargi Buhari da karya masa harkokin kasuwanci

Buhari da Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya sayar da hannun jarinsa a kamfanin Integrated Logistics Services Limited (Intels), yana mai zargin gwamnatin Buhari da neman karya kamfanin.

Mai magana da yawun jigon na jam’iyyar adawa ta PDP kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, Paul Ibe, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

Ya ce an tilasta wa Atiku ɗaukar matakin ne saboda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari “ta matsu ta karya kamfanin” tun 2015.

Atiku ya kafa kamfanin na Intels tare da wani ɗan ƙasar Italiya mai suna Gabriele Volpi, wanda yake yi wa kamfanoni ayyuka musamman na man fetur da iskar gas.

“Atiku ya sha sayar da hannun jarinsa na kamfanin Intels a baya amma abin ya yi ƙamari ne daga 2015 saboda burin wannan gwamnatin shi ne ta karya kamfanin da ke samar wa dubban ‘yan Najeriya aiki kawai saboda siyasa,” in ji sanarwar.

“Ya sayar da hannun jarinsa na Intels kuma ya mayar da kuɗinsa wasu ɓangarorin na tattalin arziki domin samun riba da samar da ayyukin yi. Ya kamata a riƙa bambanta siyasa da kasuwanci.”

A shekarar 2010 ne kamfanin ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da hukumar kula da gaɓar ruwan Najeriya ta Nigerian Ports Authority (NPA), inda zai riƙa karɓar haraji a madadin hukumar game da wasu daga cikin ayyukanta.

Sai dai a 2017 Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce yarjejeniyar ta saɓa wa doka kuma gwamnati ta soke ta.

Kazalika, an sha zargin kamfanin da ƙin biyan haraji da kuma gaza biyan dala miliyan 48 ga gwamnatin Najeriya.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt By Saxone Akhaine, Kaduna 15 May 2021   |   4:12 am   Amaechi Arewa Youths under the umbrella of...

Mata ayi hattara: Wani mazanbaci yana amfani da social media wajen yiwa mata fyaɗe kuma ya kashesu

TURKASHI: Dubun wani matashi ta cika da ya kware wajen shigar attajirai a social media yana gayyatar yan mata wajensa da sunan zai basu...

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Maigirma Gwamna Matawalle ta yi nasarar...

Rikicin Isra’ila da Falasɗinawa: Su wane ne Larabawan Isra’ila?

Rikicin Isra'ila da Falasɗinawa: Su wane ne Larabawan Isra'ila? 14 Mayu 2021 Wannan makon ya kasance mai cike da rikici a yankunan Isra'ila da Falasɗin. Bayan shafe...
%d bloggers like this: