Atiku Ya Nemi ‘Yan Nijeriya Da Su Sake Komawa Ga Allah

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a ranar Alhamis ya shawarci kiristocin Nijeriya da sauran ‘yan Nijeriya baki daya da su yi amfani da wannan lokacin na bukin kirsimeti wajen sake komawa ga Allah.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Paul Ibe ya fitar a Abuja, inda ya shawarci ‘yan kasar da su dage da addu’a, wanda ya ce ya yi imanin cewa tana da rawar da za ta taka wajen kawo zaman lafiya, hadin kai da kuma ci gaban kasa.

Atiku har wala yau ya kara da cewa; yana da kyau ‘yan Nijeriya su rungumi juna tare da nuna wa juna soyayya wajen zaman lafiyar kasa. Ya nemi ‘yan Nijeriya da su zama masu kyawawan fata da yin aikin da ya dace wajen ganin an dawo da zaman lafiya da mutuncin Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here