Yanzu na gama magana da mahaifi da mahaifiyar Munir Sada, yaron da aka ce kungiyar wasan kwallon kafa ta Arsenal ta dauka.  @Jaafar Jaafar

Ga wasu muhimman batutuwa da na samu daga tattaunawar da mu ka yi.

1) Shashen nemo yara masu nasibin kwallo ajin ’yan kasa da shekaru 9 ta “Arsenal Academy” ta zakulo Munir

2) A watan Mayun wannan shekara ne su ka je da mahaifiyarsa aka masa rajista, duk da cewa ba makarantar kwana ba ce — zuwa su ke yi ‘training’ sau biyu zuwa uku a sati.

3) Yaron shekarar sa takwas

4) Kungiyar Arsenal ba ta bawa yaro ko mahaifan yaron da ke wannan mataki kudi don sun yi masa rajista.

—————————

Sharhi:

Ba komai ne in ka gani a kafar Internet yake zama gaskiya ba. Ya kamata mu dinga tuntuba irin makamanciyar wannan idan mun ga labari a kafar da ba mai inganci ba ce.

Dabarun gane labarin gaskiya sun kunshi abinda malaman tsangayar koyar da aikin jarida ke kira “5Ws & H” (Who, What, When, Where, Why & How). A kullum mai karatu ya kamata ya duba labari da Idon basira don gano sahihancin labari. Cikar sahihin labari shi ne bayan ya kawo maka gundarin maganar da wanda abin ya shafa, to ya zo maka da yaushe abin ya faru, a ina ya faru, ta yaya ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here