Abisa ga Al’ada a kasar Zazzau, idan Sarki yayi Hawan Sallah, Daushe ko Bariki a Lokacin Damina kuma a kayi ruwan sama Sarki na Bisa Doki.
Toh kayan da yasa inya ciresu Ana kaima Sarkin Ruwan Zazzau ne kyauta daga Sarki. Toh Bana Tarihi ya mai maita kansa a zazzau.
Ranar Hawan Daushe14/5/2021 anyi ruwan sama a Zaria . Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli ya aika da sakon kaya zuwa ga Sarkin Ruwa. Kuma a jiya Sarkin ruwa yasa kaya yazo Godiya a kamar Yadda Aka saba.
Allah shi kara wa sarki lafiya
Daga Dandalin Tarihin Magabata