Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta fuskanci ƙalubale a 2023 idan har shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa.

Sanata Ahmad Lawan ya yi wannan gargaɗin ce a cikin jawabin da ya gabatar a taron matasan jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja.

“Ko mun ki mun so, gaskiya magana ita ce, goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ne APC ta samu a sassan Najeriya,” in ji shi.

Don haka ya ce dole ne jam’iyyar ta fara tanadi da shiri domin samun ɗorewar goyon bayan da ayyukan gwamnati mai ci ta hanyar tabbatar da shugabannin jam’iyyar sun miƙa mulki ga matasan da suka cacanta na jam’iyyar APC.

Shugaban majalisar dattawan ya ce Buhari na da rawar da zai taka ko da ya sauka amma kuma jam’iyyar sai ta fi fuskantar babban ƙalubale idan ya gama mulkinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here