Home Sashen Hausa ANYI GASAR FARETIN BAN GIRMA GA ANNABI (S) A KATSINA.

ANYI GASAR FARETIN BAN GIRMA GA ANNABI (S) A KATSINA.

ANYI GASAR FARETIN BAN GIRMA GA ANNABI (S) A KATSINA.

– Bin Yaqoub Katsina.
Kamar yadda duk shekara lajnar Islamiyyu ke shirya wa makarantu gasar faretin ban girma ga Annabi (S) domin nuna murna da haihuwarSa (S). Bana ma taron ya gudana a filin Atc da ke cikin garin na Katsina.

Da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Asabar 7/11/2020 taron ya soma. Taron na bana ya ƙayatar sosai musamman faretin da aka yi a muhallin ya nuna an samu ci gaba fiye da bara. Hurras sune suka fara taka faretin ban girma a matsayin mabuɗi.

Sannan ‘yan Fudiyoyi waɗanda basu cikin gasar, daga bisani kuma aka fara gasar gadan-gadan. Bana dai an kasa gasar ne zuwa kaso biyu. Kaso na farko na ƙaramin mataki, wanda a nana Madratul Irshadu-subyan D/Amare ta zo na ɗaya, sannan sai na biyu na manya makarantu shi kuma a nan Tahriƙul Islam tazo na ɗaya.

Daga ƙarshe Shaikh Yakubu Yahaya Katsina yayi jawabin rufewa bayan ya kammala amsar dukkan faretin (gaisuwa) ga ɗalibban da Harisawa. A jawabin Malamin yayi kira da Musulmi su haɗe kansu, sannan ya ƙara jadadda la’anta da Allah wadai kan ɓatancin da Macron na kasar faransa yayi wa Annabin rahama (S).

Anyi taron lafiya an tashi lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: