Advert
Home Sashen Hausa Antsinci gawar Shugaban Jam'iyyar APC na jihar Nasarawa jim kaɗan bayan sace...

Antsinci gawar Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Nasarawa jim kaɗan bayan sace shi da akayi

An tsinci gawar shugaban APC da aka sace a daren Asabar

Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari

An tsinci gawar shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa

– Wata majiya ta kusa da iyalansu, ta shaida wa manema labarai hakan a ranar Lahadi

– Duk da dai har yanzu jam’iyyar APC bata riga ta ce komai ba a kan lamarin

An tsinci gawar shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, bayan an yi garkuwa da shi.

Watamajiya da take kusa da iyalan mutumin ne ta sanar da jaridar PREMIUM TIMES a ranar Lahadi da rana.

Sannan wani shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, wanda bai so a ambaci sunansa ba, shi ma ya tabbatar da mutuwar.

Duk da dai har yanzu jam’iyyar APC ba ta riga ta yi magana ba a kan garkuwa da shi da aka yi ba.

Shugaban karamar hukumar Karu, Samuel Akala, ya tabbatar da mutuwar a shafinsa na sada zumuntar zamani ta Facebook.

Dama PREMIUM TIMES ta sanar da garkuwa da Shekwa da aka yi a ranar Asabar a gidansa da yake Lafia.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa, Dele Longe, ya tabbatar da garkuwa da shi da aka yi da safiyar Lahadi.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

DRAFT APC CONVENTION TIMETABLE – Jan 16, 2022

1. January 17th - PMB Letter to CECPC on February National Convention and associated matters 2. January 18th -CECPC Meeting announcing National Convention date of...

Da ƊUMI-ƊUMI- Kotu ta umarci Rundunar Sojin Ƙasa da ta baiwa Nnamdi Kanu Naira biliyan 1

Wata Babbar Kotu da ke zaman ta a Umuahia ta baiwa Gwamnatin Taraiya da Rundunar Sojin Ƙasa da su baiwa Jagoran masu Rajin Samar...

THE RECONSTRUCTION OF THE APAPA – OWORONSHOKI – OJOTA EXPRESSWAY IS PROGRESSING EXPRESSLY!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/258361216380403/

Teenager kills man over football league supremacy

Teenager kills man over football league supremacy By Danjuma Michael, Katsina 19 January 2022   |   2:53 am A teenager, Idris Yusuf, 18, has allegedly killed a...