Home Sashen Hausa Ansoke Rindunar SARS a Najeriya

Ansoke Rindunar SARS a Najeriya

SARS: An soke rundunar fashi da makami a Najeriya

.

Babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami a Najeriya wato SARS.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabin kai tsaye ga manema labarai a ranar Lahadi.

Soke rundunar ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasar, inda ko a yau Lahadi sai da aka yi irin wannan zanga-zangar a Ingila.

‘Yan ƙasar dai suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da saɓa dokokin aiki.

A baya dai gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta soke rundunar ba, sai dai ta yi mata sauyi ko kuma kwaskwarima kan yadda rundunar ta ke gudanar da ayyukanta, inda ko a kwanakin baya sai da Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Ahmed Lawan ya ce ba zai yiwu a soke rundunar ba sai dai a sauya tsarinta.

Hakazalika wasu daga cikin ƙusoshin gwamnatin ƙasar da wasu gwamnoni da muƙarraban shugaban ƙasar na da irin wannan ra’ayi.

Me matakin soke SARS ya ƙunsa?

A jawabin da Babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya ya yi ga manema labarai a ranar Lahadi, ya bayyana cewa an soke rundunar SARS da ke aiki a duka jihohin Najeriya 36, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa duka dakarun da ke aiki a ƙarƙashin rundunar da aka rushe za a rarraba su zuwa sauran rundunoni daban-daban domin gwama su tare da sauran ‘yan sanda na Najeriya.

Game da yaki da fashi da makami a faɗin ƙasar, babban sifeton ‘yan sandan ya ce ba da daɗewa ba za a fito da wani sabon tsari.

Ya kuma ce za a kafa wani kwamiti na musamman da zai ƙunshi ‘yan Najeriya da masu ruwa da tsaki da zai bayar da dama ga ‘yan ƙasar su rinƙa bayar da shawara ga hukumar ‘yan sandan kan abubuwan da ke ci wa jama’a tuwo a ƙwarya.

A ɓangaren gudanar da bincike kan cin zarafi da aka yi wa ‘yan ƙasa kuma, babban sifeton ‘yan sandan ya bayyana cewa za a kafa wani kwamitin bincike wanda zai ƙunshi ƙungiyoyi masu zaman kansu kuma ya yi alƙwarin za a hukunta waɗanda aka samu da laifi.

Me ya sa aka soke SARS

Wannan zanga-zangar dai ta fara ne tun tuni a shafin Twitter, inda a duk lokacin da aka samu rikici tsakanin SARS ɗin da wasu ‘yan ƙasar, akan tattauna mau’du’in #ENDSARS a shafin Twitter. Da an tattauna na kwana biyu, sai kuma maganar ta mutu.

Sai dai a baya bayan nan da alama tura ta kai bango, sakamakon zanga-zangar da aka shafe lokaci ana yi a Twitter ta sa mutane suka fara fitowa kan tituna suna gudanar da zanga-zangar.

Garuruwan Abuja da Legas ne kan gaba wurin wannan zanga-zangar inda daga baya jihohi kamar irin su Oyo da Kaduna da dai sauransu suka biyo baya.

Daga cikin manyan fuskokin da ake gani wuri jagorancin wannan zanga-zanga akwai Aisha Yessufu, wata ‘yar gwagwarmaya a Najeriya da kuma Babban Editan Jaridar Sahara Reporters wato Omoyele Sowore.

Duk da matsin lamba da barazana da wasu daga cikin masu zanga-zangar suke samu yayin da suke tattaki, hakan bai sa sun daina ba.

Ko a jiya sai da aka harbe wani a Ogbomosho da ke jihar Oyo a zanga-zangar.

Kuma kusan kullum idan masu zanga-zangar suka fito, ‘yan sandan sukan yi ƙoƙarin tarwatsa su ta harba musu hayaƙi mai sa hawaye da harbin bindiga.

Amma a ‘yan kwanakin nan, kullum masu zanga-zangar ƙaruwa suke yi, kuma da alama har sun saba da irin barazanar da ‘yan sanda ke yi musu wanda hakan ya sa ma suka daina guduwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: