Advert

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

Makarantar Kagara

An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma’aikata guda 41 da ‘yan bindiga suka sace a Jihar Neja.

Wani jami’in gwamnatin jihar ne ya tabbatar wa da BBC Hausa sakin nasu, inda ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa Minna, babban birnin jihar.

Ya zuwa yanzu babu wani ƙarin bayani game da ko an biya kuɗin fansa kafin sakin mutanen.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya nuna yadda mutanen suka galabaita, sun yi zaman daɓaro a ƙasa bayan sakin nasu.

Ranar Laraba, 17 ga watan Fabarairu ne wasu ƴan bindiga suka sace mutum 41 daga makarantar kwana ta maza zalla da ke Kagara a Ƙaramar Hukumar Rafi.

Ɗalibai guda 27 ne a cikin waɗanda aka sace ɗin, sai malamai da iyalansu da kuma ma’aikata guda 14.

‘Yadda ‘yan fashin suka shigo makarantarmu’

Makarantar Kagara

Wani ɗalibi da ya tsira daga harin ‘yan bindigar na ranar 17 ga watan Fabarairu ya bayyana wa BBC yadda lamarin ya faru da tsakar dare.

Ya ce kimanin ƙarfe 2 na tsakar daren ranar ta Talata wani daga cikin abokansa ya tashi domin yin fitsari, sai ya lura da wasu mutane na dosowa makarantarsu ta baya riƙe da fitulu suna haskawa.

“A lokacin ne sai abokin nawa ya tashe ni yake ce min ga wasu mutane can suna nufo mu ta bayan makaranta, bai san ko su wanene ba, mu fita mu gani, sai nace masa a’a, kada ya ji tsoro ya koma ya kwanta, sai ya ƙi, ya ɗauki fitila ya haska musu, da suka ga an haska su sai suka yi sauri suka kashe nasu fitilun” a cewar ɗalibin da muka sakaye sunansa.

Ya ƙara da cewa “har lokacin da suka shigo bamu san ɓarayin mutane bane, sai suka ka fara tayar da dalibai daga barci suna ɗora musu bindiga, suna cewa duk wanda ya yi motsi ko ihu za su kashe shi nan take, to a lokacin ne wani ɗalibi ya lura miyagu ne, sai ya ƙwalla ihu ya ce kowa ya gudu ɓarayi sun shigo, abin da ya sa mutane suka fara fita suna ta guduwa.

”Wani abokina ma munyi sallama da shi zai je ya kwanta, ya tafi kenan ya yi karo da su, juyowar da zai yi zai tsallaka taga ya gudu, sai suka buɗe masa wuta tare da yi masa harbi uku, ɗaya a kansa, ɗaya a baya ɗaya kuma a ciki, har sai da kwanyar kansa ta zazzago waje” inji shi.

Ɗalibin ya ce ya ɓuya ne tare da wasu abokansa su 10 a wani lungu a wurin kwanan su, wanda hankalin ƴan bindigar bai kai wajen ba, duk da sun riƙa zazzagayawa ta wajen suna duba ko akwai mutane.

”Abun da ya bani tausayi ya kuma bani haushi shine yadda a gabana aka kashe abokina, ga gawarsa a gabana ina kallo, na yi kukan baƙin ciki, iyayena suna ta cewa in yi haƙuri’ a cewar wannan ɗalibi.

Ya ce maharan sun shiga makarantar ne sanye da kayan sojoji dukkaninsu, kuma sun shafe kusan awa uku kafin su tafi da mutanen da yawansu ya kai aƙalla 50, da wani malami guda ɗaya, da iyalan shi mutum shida.

Ko da BBC ta tambaye shi ko a kan me maharan suka zo?, sai ya ce basu zo da babur ko ɗaya ba, da ƙafa suka tako tun daga nesa, sannan ko da suka kwashe ɗaliban a ƙafa suka juya suka tafi da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: