Ankashe sama da mutum shabiyar a karamar hukumar faskari.

Sama da mutum goma sha biyar aka kashe a harin jiya talata,karamar hukumar faskari

Harin Dan’aji Karamar hukumar Faskari: Mahara sun kashe sama da mutum 15 a jiya

Sakamakon harin yan ta’addan daji da Katsina Daily Post News ta rawaito maku cewa ana cikin kaiwa a garin Dan’aji yankin Yarmalamai dake cikin karamar hukumar Faskari a yanmacin jiya Talata, kawo yanzun mun sami labarin cewa an tsinto gawarwakin mutum 15 da aka tabbatar maharan sun kashe, a inda kuma wata majiyar ta rawaito mana cewa sama da mutum 16 ne aka ga gawarwakin nasu a yau Laraba.

Bayan asarar dukiyoyi kuma an sami labarin bacewar wasu yan garin da alhalin yanzun ba a san inda suke ba.

Yan ta’addan dajin sun shiga garin tun da wajen misalin karfe 6 na yammar jiya inda sukai ta cin karensu babu babbaka har wajen 8pm na dare, kamar yadda yan yankin suka sheda wa Katsina Daily Post News.

Duk da rundunar tsaro ta Sahel Sanity da aka kafa a garin Faskari domin yakar yan ta’addan yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, har yanzun maharan ba su daina shiga garuruwan dake yankin karamar hukumar Faskarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here