Ankama wasu masu haƙar ƙabari suna sace sassan jikin mutane

INDA RANKA: A daren Jiya 22/04/2021 misalin karfe 10 zuwa 11 na dare dubun wasu mutane biyu dake haƙe Kabarin bayin Allah domin daukan sassan jikin su a Maƙabartan mu ta Nassarawa da Sabon Gari Kaduna wacce ke bayan IBBI ya cika.

Daga Aminu Ladan Tela

Waɗannan mutane mazauna Garin Kabala west ne dake yankin ƙaramar hukumar Igabi.

Tsohon sunan shi Abdulazeez kamar yadda ya bayyana, matashin kuma sunan shi Ahmad dukkanin su Ƴan Jahar Kwara ne.

Yanzu haka su na hannun Ƴan Sanda domin cigaba da bincike.

Allah ka ƙara tona asirin irin waɗannan mutane a duk inda suke alfarman wannan wata mai albarka🤲😭

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here