Advert
Home Sashen Hausa Ankai hari a gidan ɗan majalisar tarayya Yahaya kusada

Ankai hari a gidan ɗan majalisar tarayya Yahaya kusada

Wan’nan shine Suleman da aka sace a gidan

AN KAI HARI GIDAN DAN MAJALISAR TARAYYA YAHAYA KUSADA.

muazu hassan  @katsina city city news

A daren jiya asabar 21/11/2020 da misalin karfe daya na dare wadansu mahara da ba a San ko su waye ba.suka kai Hari gidan Dan majalisar tarayya mai wakiltar kusada,kankia da ingawa da ke jahar katsina ,
Maharan da ba san adadin yawansu ba. Sun kai harin ne a gidan Dan majalisar dake garin kusada karamar hukumar kusada a jahar katsina.
Maharan sun tafi da ma aikatan gidan biyu wata mata mai suna Talatu da wani matashi mai suna Suleman.
An tabbatar mana da cewa, an sanar da jami an tsaro kuma sun je gidan sun dau bayanan abin da ya faru.
Mun kuma samu labarin a daren jiya, wasu maharan sunyi ma wasu yan sa kai a karamar hukumar kurfi kofar raggo suka halaka uku daga cikin su.
Mun samu labarin cewadaukin da jami an tsaro suka kai cikin gaggawa shine ya rage barnar wadanda akayi ma kofar ragon.
________________________________________________
Katsina city news na a bisa yanar gizo na www.katsinacitynews.com da bisa shafin Facebook page .Facebook group. Twitter, Instagram , you tube TV da sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: