An kai ƙarar shugaban INEC Kotu

Bbc

An buƙaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar da’ar ma’aikata ta fito ta bayyana kadarorin shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa wato INEC, Mahmood Yakubu.

Jaridar The Cable a Najeriya ta rawaito wanda ya gabatar da karar, Emmanuel Agonsi, a wasikar da ya aikewa hukumar, yana bukatar shugaban INEC da ƴaƴansa da basu da aure su bayyana kadarorinsu.

Agonsi na son cikakkun bayanai kan dukiyar Yakubu daga shekara ta 2007 zuwa 2012 lokacin da yake rike da shugabancin asusun bada tallafin karatun makarantun gaba da sakandare wato TETFUND da zamansa a hukumar INEC tsakanin 2015 zuwa 2020.

Ya kuma buƙaci kotun ta umarci hukumar da’ar ma’aikata, ta fitar da bayanai kan kayayyaki da dukiyoyi Yakubu da ƴaƴansa na tsawon wadanan shekaru, a cewar The Cable

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here