An kafa rundunar da za ta maye gurbin SARS a Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kafa wata sabuwar runduna da za ta maye gurbin SARS, wadda aka rusa bayan an kwashe kwanaki ana zang-zanga.
Wata sanarwa da Kakakin ‘Yan Sanda Frank Mba ya aike wa manema labarai a yau Talata ta ce Sufeto Janar Mohammed Adamu ya kafa rundunar Special Weapons and Tactics (SWAT).
“An kafa rundunar ne domin cike gurbin abin da zai biyo bayan rushe SARS,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ce za a yi wa dakarun sabuwar rundunar ta SWAT gwaje-gwajen lafiyar ƙwaƙwalwa domin auna lafiyarsu kafin ɗaukarsu aikin sannan kuma za su fara karɓar horo a mako mai zuwa.