Gwamnatin Jihar Katsina Ta Kaddamar Da Cibiyar Ayyukan Hadin Gwiwar Hukumomin Tsaro da Sadarwa, watau “Security Agencies Joint Operations And Communication Center” a Jihar Katsina.
Ofishin Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara na musamman akan harkokin tsaro Alh. Ibrahim Katsina hadin gwiwa da “Gafai communication Katsina” kalkashin jagorancin Alh. Musa Yusuf Gafai suka assasa wannan cibiya, Gwamnatin Jihar Katsina kalkashin jagorancin Rt. Hon. Aminu Bello Masari ta dauki nauyin kafa wannan cibiya domin taimaka ma aikin samar da tsaro a Jihar, an tsara cibiyar bisa fasahohin sadarwa na zamani.
Cibiyar ta shafi dukkan hukumomin tsaron da muke dasu a Jihar Katsina, kuma kowace hukumar tsaro tana da wakilci na jami’inta a cibiyar, an kafa wannan cibiya domin isar da sako ga hukumomin tsaro da Gwamnati cikin sauki, idan an samu wata barazana ta tsaro a cikin Jihar Katsina, Ranar Juma’a 25/06/2021 Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Aminu Bello Masari ya kaddamar da cibiyar a hedi kwatar rundunar ‘Yan Sanda ta Katsina dake kan hanyar zuwa Daura.
Da yake gabatar da jawabin shi yayin da yake kaddamar da cibiyar Mai girma Gwamnan ya yi kira ga Al’ummar Jihar nan na ciki da wajen Jihar Katsina, dasu shigo domin bada gudumuwarsu don ganin an kawo karshen matsalar tsaron da Jihar take fama dashi, domin matsala ce data shafi kowa da kowa.
Gwamnan ya cigaba da cewa” masu aikata aikin ta’addancin nan babu ruwansu da jam’iyyar da kake ko addini kake, ko kabilar da kake, aikin ta’addancinsu ya shafi kowa, ya zama wajibi mu tashi tsaye mu hada kai mu tunkarin wannan matsala domin ganin bayanta, Jami’an tsaron Sojoji da ‘Yan Sanda kadai ba zasu iya bamu tsaro ba, sai mun taimaka masu.
Tunda farko da yake gabatar da jawabin shi, Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan harkokin tsaro Alh. Ibrahim Katsina ya bayyana cewa” kafa wannan cibiya zai taimaka kwarai da gaske wajen aikin samar da tsaro a Jihar Katsina, daga karshe ya godema Mai girma Gwamna Aminu Bello Masari akan yadda yake bada cikakken goyon baya da gagarumar gudumuwa akan aikin samar da tsaro a Jihar Katsina.
Daga karshen taron kaddamar da cibiyar an bada wayoyin hannu na musamman ga shugabannin hukumomin tsaro na Jihar Katsina baki daya, haka zalika an bada wayoyin ga masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro na bangaren Gwamnati, tun daga Gwamna, sakataren Gwamnati, shugaban Ma’aikata na gidan Gwamnati, mai baiwa da Gwamna Shawara akan Harkokin tsaro, manufar shirin domin samun sako na barazanar tsaro cikin sauri yadda za’a dauki mataki cikin gaugawa.
Taron ya samu Halartar dukkan shugabannin hukumomin tsaro, Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Katsina wanda ya samu wakilcin shugaban Kwamitin kula da harkokin tsaro na Majalisar, Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dutsinma Hon. Muhammad Abubakar Khamis , sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa, shugaban Ma’aikata na gidan Gwamnatin Jihar Katsina Alh. Muntari Lawal, yan majalisar zartarwa ta Jihar Katsina, Babban Jojin Jihar Katsina Mai Shara’a Musa Danladi Abubakar, Alkalin Alkalai na jihar Katsina. Dadai sauransu.
Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
26, June 2021.