AN GUDANARA DA JANA’IZAR NURA DAHIRU MANGAL.

Tuni dai aka gudanar da jana’izar Nura Dahiru Mangal, a babban Dan kasuwar nan na jihar Katsina Alhaji Dahiru Bara’u Mangal.
An gudanar Sallar gawar marigayin ne a farfajiyar Masallacin Juma’a na Tayoyi a nan cikin birnin Katsina.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Katsina Imam Gambo Mustapha shine ya jagoranci Sallar wadda ta samu halartar dumbin mutane daga Ciki da wajen jahar nan.
Bayan kammala sallatar Marigayin an rufe shi a Makabartar Danmarna dake garin Katsina.
Nura Dahiru Mangal dai ya rigamu gidan gaskiya ne sakamakon hatsarin Babur da ya ritsa da shi a ranar Larabarda ta gabata a kusa da Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Hassan Usman dake Katsina.
Allah yayi mashi rahama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here