A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, mai shekaru 90 a duniya, ya gwangwaje da amaryar sa, Aisha Iro Maikano, ƴar shekara 20 da haihuwa.

Sarkin, wanda a ka haife shi a shekarar 1921, ya angwance da sahibar ta sa ne a wani ƙwarya-ƙwaryar biki, bayan da su ka ɗauki gajeren lokaci su na soyayya.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa angon ya biya sadaki naira miliyan 1, lakadan ga amaryar, wacce ƴar gidan Fagacin Katsina, Iro Maikano ce.

Wata majiya ta tseguntawa jaridar cewa Sarkin na da auri-saki kuma ya auri ƴan mata 4 a shekaru 6 da suka gabata.

A wani taƙaitaccen fefen bidiyo, an nuno amarya baki har kunne tana raƙashewa, inda ta ke rawa bayan da a ka kunna kiɗan gargajiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here