An gano wani gidan garkuwa da mutane a cikin ramin kwalbati, ciki har da AC da janareto

Abun al’ajabi ya faru a unguwar Orile dake jihar Lagos bayan da magidanta suka bankado wani rami (kwalbati) da ake zargin wajen da masu garkuwa da mutane suke amfani dashi ne wajen sace mutane suna boyewa.

A cikin ramin an samu mutane da kayan makarantar yara dayawa da kuma Injin janareto da injin sanyaya daki wato AC da dai sauran kayan sanyaya daki.

Tuni dai mazauna unguwar suka kashe wanda suka kama a ciki a yayinda suka kubutar da wadanda aka boye a cikin ramin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here