An dakatar da kamfanonin waya sayar da sabbin layuka a Najeriya

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya Nigerian Communications Commission (NCC), ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin dakatar da sayar da sabbin layukan wayar salula a ƙasar.
Cikin wata wasiƙa da ta aike wa kamfanonin ranar Litinin wadda kuma jaridar TheCable ta gani, hukumar ta ce ta duƙufa ne kan duba rumbun bayanan rajistar masu layukan, kuma umarnin zai ci gaba da aiki har sai an kammala.
“Bisa umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na tabbatar da an bi tsarin yi wa layuka rajista, hukumar ta duƙufa kan tantance rajistar masu layuka domin ta tabbatar da an bi umarnin sannan ta daidaita ayyuka,” a cewar wasiƙar da daraktan ayyuka na NCC, A.I. Sholanke, ya sanya wa hannu.
“Saboda haka, an umarce ku da ku dakatar da sayarwa da kuma ƙaddamar da sabbin layukan kamfaninku har zuwa sanda za a kammala binciken.
“Sai dai kuma idan ya zama dole, za a iya bayar da umarni na musamman idan an samu amincewar gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NCC.”
Wasiƙar ta kuma gargaɗi kamfanonin cewa idan suka ƙi bin umarnin “za a iya ƙwace lasisin gudanar da ayyukansu”.
Daraktan hulɗa da jama’a na NCC, Ikechukwu Adinde, ya faɗa a yau Laraba cewa matakin ya zama dole saboda “yadda layuka marasa rajista suka karaɗe gari, waɗanda ake amfani da su wurin aikata mugayen laifuka”.