Ana zaman fargaba a jihar Kwara bayan da wani jami’in gwamnati ya mutu a ofishin sa.

Ma’aikata a ma’aikatar gona da cigaban karkara a gwamnatin jihar Kwara sun fada cikin fargaba sakamakon samun gawar wani Daraktan ma’aikatan a ofishin sa.

Darakatan, wanda aka bayyana shi mai suna Khalid Ibrahim Ndaman, darakta ne a sashen likitocin dabbobi na ma’aikatar Gona da cigaban kauyaku na jihar Kwara.

An rawaito cewa marigayin lafiyar sa kalau, anma koda wani daga cikin ma’aikata a ma’aikatar ya kwankwasa kofar ofishin sa yaji shiru ba’a amsa masa ba yana shiga ofishin sai ya sami gawar sa a cikin ofishin.

“Akwai sauran ayyukan da suka rage ba’a kammala su ba tun ranar Juma’a wadanda ake bukatar a kammala su tare da shi”

“Bayan ya jira a waje daraktan bai amsa masa ba, Ma’aikacin ya shiga cikin ofishin yana shiga ya same shi ya kifa kansa akan tebur.”

Majiyar mu ta kara tabbatar mana da cewar; “Ma’aikacin ya gaishe shi bai amsa ba har sai da ya matsa kusa da shi ya taba jikin sa daga nan ya gane cewa ya riga ya mutu”

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kwara, Ajayi Okesanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace “Ina da masaniya akan faruwar lamarin. Mutuwa ce da ta faru yanzu kwatsam sai mun kammala binciken mu za mu yiwa manema labarai cikakken bayanin abinda muka gano” Inji Ajayi Okesanmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here