Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa an gano wata sabuwar nau’in cutar korona B.1.640.2 wanda aka sa wa sunan ‘IHU’ a kasar Faransa.

Kungiyar ta ce tun a watan Nuwanba 2021 ne aka gano cutar a kudancin Faransa a jikin wani dan kasar wanda ya yi allurar rigakafi kuma ya dawo daga kasar Kamaru.

Masu gudanar da bincike sun ce basu da masaniya game da cutar amma cutar ta fi nau’in Omicron yaduwa domin tana iya rikiɗa sau 46 fiye da Omicron.

Zuwa yanzu mutum 12 ne ke dauke da cutar kuma babu wani da ya rasu a cikinsu.

WHO ta ce nau’in Omicron ta yadu zuwa kasashe 128 sannan yana daga cikin dalilan da ya sa kasashen duniya ke Kara samun yawan mutanen dake kamuwa da cutar korona.

Najeriya

Alkalumar yaduwar cutar korona da hukumar NCDC ta fitar daga ranar Litini zuwa Alhamis ya nuna cewa mutum 2,745 ne suka kamu da cutar sannan mutum 27 sun mutu a Najeriya.

Hukumar ta ce Najeriya ta ci gaba da samun karuwa a yaduwar cutar da yawan mutanen dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar musamman yadda aka gano sabbin nau’ikan cutar Omicron da IHU.

A ranar Litini mutum 670 ne suka kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum shida a jihohi 7.
Mutum 8 sun mutu sannan mutum 428 sun kamu ranar Talata a jihohi 13 da Abuja.

A ranar Laraba mutum 856 ne suka kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 5.

A ranar Alhamis mutum 8 sun mutu mutum 791 sun kamu a jihohi 13 da Abuja.

Hukumar ta kuma ce akwai mutum 249 da suka kamu da cutar ranar 5 ga Janairu 2022 a jihar Legas da aka hada a cikin mutum 791 din da suka kamu da cutar a kasar nan.

Zuwa yanzu mutum 246,195 ne suka kamu, an sallami mutum 217,509 sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,066.

Har ya zu akwai mutum 25,620 dake dauke da cutar a Najeriya.

Gwamnati ta ci gaba da yin kira ga mutane da su gaggauta yin allurar rigakafin cutar tare da ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Yaduwar cutar

Legas – 96,305, Abuja-27,560, Rivers-10,930, Kaduna-10,213, Filato-10,209, Oyo-10,083, Edo-7,576, Ogun-5,747, Kano-4,828, Akwa-ibom-4,566, Ondo-4,998, Kwara-4,015, Delta-4,446, Osun-3,123, Enugu-2,824, Nasarawa-2,648, Gombe-2,695,

Katsina-2,367, Ebonyi-2,048, Anambra-2,424, Abia-2,029, Imo-2335, Bauchi-1,896, Ekiti-1,931, Benue-2,109, Barno-1,577, Adamawa-1,136, Taraba-1,254, Bayelsa-1,303, Niger-1,077, Sokoto-810, Jigawa-642, Yobe-501, Cross-Rivers-662, Kebbi-458, Zamfara-348, da Kogi-5.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here