Ana sa ran Shugaba Buhari za a fara yi wa rigakafin korona a Najeriya

Getty Images

Nan gaba a yau ne ake sa ran zuwan kashin farko na allurar riga-kafin cutar korona kusan miliyan huɗu zuwa Nijeriya, ƙarƙashin shirin COVAX mai samar da riga-kafin ga ƙasashe matalauta.

kamar yadda aka saba fara yi wa shugabannin kasashen da aka kai wa rigakafin, a Najeriya ma ana sa ran Shugaba Buhari za a fara yi wa, sannan manyan muƙarraban gwamnati da kuma jami’an kiwon lafiya da ke kan gaba wajen yaki da wannan annoba.

Tuni dai gwamnatin ta ƙaddamar da tsare-tsaren da za su tabbatar da rabon allurar bayan ta karɓi wannan kashi na farko.

Zuwan riga-kafin zai kawo ƙarshen jiran da aka yi tun daga ƙarshen watan Janairu, na samun allurar a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here