Advert
Home Sashen Hausa Ana bincike kan yadda 'Fafaroma ya so' hoton wata mai tallan kayan...

Ana bincike kan yadda ‘Fafaroma ya so’ hoton wata mai tallan kayan ƙawa mai shigar banza a Instagram

Ana bincike kan yadda ‘Fafaroma ya so’ hoton wata mai tallan kayan ƙawa mai shigar banza a Instagram

FafaromaCopyright: EPAVATICAN MEDIA HANDOUT

Fadar Vatican ta ce tana bincike bayan da shafin Fafaroma Francis ya latsa alamar son hoton wata mai tallan kayan ƙawa mai shigar banza ƴar Brazil a Instagram.

Babu tabbas kan lokacin da aka yi amfani da shafin Fafaroman wajen latsa alamar son hoton na Natalia Garibotto, da take sanye da kayan makaranta.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kafofin yaɗa labarai suka fara bayar da rahotannin batun, kafin daga bisani aka je aka goge alamar son da aka latsa a kan hoton.

Jami’an Fadar Vatican a yanzu suna bincike kan yadda irin haka ta faru da shafin Fafaroma.

Mai magana da yawun ofishin Fafaroma ya shaida wa BBC cewa “a iya saninmu ba Fafaroma ne ya danna alamar son hoton ba.”

Fadar Vatican na aiki da kamfanin Instagram don gano ta yadda abin ya samo asali, kamar yadda ya ƙara da cewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Babu wanda zai bar jami’a saboda bai biya kuɗin makaranta ba -Farfesa Muhamad Sani Tanko

Babu wanda zai bar jami'a saboda bai biya kuɗin makaranta ba – Farfesa Muhammad Sani Tanko, Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna ya kawar da tsoron da iyayen...

Police Arrest 60-Year-Old Man Conveying Rifles In Car Bonnet

A 60-year-old man, Umar Muhammed, was arrested while conveying firearms across the country. The suspect uses his vehicle to transport rifles concealed in the bonnet...

TABBAS ZA AYI ZABEN SHUGABANNIN APC …inji bagudu

TABBAS ZA AYI ZABEN SHUGABANNIN APC ...inji bagudu @katsina city news Gwamnan jahar kebbi bagudu ya tabbatar ma da Manema labarai a Abuja cewa tabbas za...
%d bloggers like this: