Wasu gungun Malamai a Kano sun bada sanarwar sauke shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil daga mukaminsa, a cewarsu ya afkar da kungiyar cikin siyasa dumu dumu.

Haka kuma, Malaman na zargin Sheikh Khalil da yin fadan babu gaira babu dalili da Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Khadimoul Islam.

A saboda haka, Malaman suka bayar da sanarwar nada Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin sabon shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here