An yi wa Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman allurar riga-kafin korona

Copyright: Saudi Gazette
An yi wa yarima mai jiran gado kuma ministan tsaro na Saudiyya, Muhammad Bin Salman allurar riga-kafin korona a ranar Juma’a.
Jaridar Saudi Gazette ta ƙasar ta ruwaito ministan lafiya na ƙasar Dakta Tawfiq Al-Rabiah inda yake gode wa yariman kan ƙoƙarin da yake yi wurin ganin cewa ƴan ƙasar sun samu riga-kafin.
A ranar 17 ga watan Disamba ne aka ƙaddamar da riga-kafin a Saudiyya inda aka fara ta kan ministan lafiya na ƙasar