An Yi Nasarar Kuɓutar Da Ma’aikatan Gonar Obasanjo

Blueink News Hausa

Rahotanni daga Jihar Ogun na bayyana cewar Kwanaki uku bayan sace ma’aikatan gonar tsohon shugaban kasa Obasanjo, rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta ceto ma’aikatan daga ramin masu garkuwa da mutane.

An ruwaito cewa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba.

An tattaro cewa ya bayyana cewa Jami’an da ke yaki da masu yaki da garkuwa da mutanen sun kasance suna bin sawun masu garkuwar, inda ya kara da cewa rundunar ta ci gaba da kakkabe jeji a kewayen yankin tun lokacin da lamarin ya faru.

“Eh, mun matsawa masu garkuwa da mutanen. Tun ranar (Alhamis) jami’anmu masu yaki da garkuwa da mutane suke cikin daji suna nemansu. “Sun sami damar gano su cikin daji a bayan Kwalejin Day Waterman, a kan hanyar Kobape. A wannan maraice, sun sake su (wadanda abin ya shafa) ba tare da sun ji rauni ko biyan kudin fansa ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here