AN YI FADA TSAKANIN KWASTAM DA MUTANEN JIBIA

Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia

Rikici ya barke tsakanin kwastan da mazauna Magamar Jibia

Da misalin karfe 1 na daren ranar Juma’a, Hukumar Kwastam ta shiga garin Magamar Jibia da ke cikin Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina don karbar kayan da ’yan kasuwa ke yin fataucinsu ba bisa ka’ida ba, daga kasashen waje zuwa Nigeria.

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa Hukumar ta Kwastam ta sha wahala sosai daga mutanen garin, biyo bayan zanga-zangar da mutanen garin suka yi yayin da kwastan din ke kokarin bude shaguna a garin.

Amma har zuwa yanzu ba mu da tabbacin ko sun debo kayan ko a’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here