An yanke wutar gidan marigayi Shehu Shagari saboda bashi

Hukumar rarraba wutar lantarki a Kaduna ta yanke wutar gidan tsohon marigayi Shehu Shagari saboda bashin naira miliyan 6 da ake bin gidan.
A ranar 28 ga watan Disamba 2018 tsohon shugaban ya rasu yana da shekara 93.
Jaridar DAILY NIGERIA a ƙasar ta rawaito kakakin kamfanin, Abdulaziz Abdullahi na cewa ba a biyan kuɗin wutar tun bayan mutuwar marigayi Shagari.
Kakakin ya kuma shaida wa jaridar cewa an basu wa’adi ko ɗaga musu ƙafa domin biyan kuɗaɗen da ake bin su kafin a yanke wutar.
Wani jami’in gwamnatin Sokoto wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce babu adalci idan aka ɗaurawa gwamnati laifi kan yanke wutar, a cewar Jaridar.