An yanke wa ‘yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana

Wasu 'yan Najeriya

‘Yan Najeriya biyu za su fuskanci da hukuncin kisa ta hanyar rataya a ƙasar Ghana muddin suka kasa ɗaukaka ƙara a cikin kwana 30 daga yau Juma’a.

Babbar Totu a Sekondi ta yanke wa Samuel Udoetuk Wills da John Oji hukuncin kisa sakamkon samun su da aikata laifin ɓatarwa da kuma kisan wasu ‘yan mata ɗalibai a Takoradi.

Mai Shari’a Richard Adjei-Frimpong wanda ke jagorantar zaman kotun daukaka kara a Ghanar ne ya karanta hukuncin a yau, yayin da sauran masu taimaka masa su bakwai suka same su ta aikata laifin na kisan ‘yan matan Takoradi guda huɗu.

Bacewar ‘yan matan Takoradin ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye kafafen yaɗa labaran a Ghana a shekarar 2018 bayan da iyayen ‘yan matan suka kai ƙara caji ofis.

Hakan kuma ya haifar da gagarumar zanga-zanga da kuma gangami a kafafen yaɗa labaran yankin kan bukatar a nemo duk inda ‘yan matan da aka sace suke.

Bayan tsananta bincike ne kuma ‘yan sandan Ghana suka gano kwarangwal ɗin wasu daga cikin ‘yan matan a cikin tankin dagwalo na karkashin ƙasa..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here