Home Sashen Hausa An yanke wa ƴar fafutukar Saudiyya hukuncin ɗaurin shekara 5 a gidan...

An yanke wa ƴar fafutukar Saudiyya hukuncin ɗaurin shekara 5 a gidan yari

An yanke wa ƴar fafutukar Saudiyya hukuncin ɗaurin shekara 5 a gidan yari

Loujain Al-Hathloul

Kafofin yaɗa labaran Saudiyya sun ce wata kotu a ƙasar ta yanke wa ƴar fafutukar nan ta ƙasar, Loujain Al-Hathloul hukuncin ɗaurin shekara biyar da wata takwas a gidan yari bisa tuhumarta da “ta’addanci”.

A cewar rahotanni, Kotun Hukunta Masu Aikata Miyagun Laifuka ta ɗaure Al-Hathloul kan tuhumar ta da laifukan da suka shafi zuzuta kawo sauyi a mulkin ƙasar da kuma ƙoƙarin ɗora ƙasar kan al’adu na wasu ƙasashe.

An kama Ms Al-Hathloul ne kwanaki kaɗan kafin bayar da dama ga mata a Saudiyya su fara tuƙin mota, wanda wannan na daga cikin fafutikar da Ms Al-Hathloul ɗin da wasu da aka kama suka daɗe suna neman a tabbatar.

A kwanakin baya danginta sun bayyana cewa ana azabtar da ita a gidan yarin da aka tsare ta, lamarin da ƙasar ta Saudiyya ta musanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...

Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of...

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...
%d bloggers like this: