Majalisar Dattawa ta Gargadi Hukumar Kwastam: dokar ƙasa ta baku damar kama kayane Kilometer Arba’in da Iyakokin Najeriya….

Majalisar Dattijai ta Umarci Hukumar Hana fasa ƙwabri ta ƙasa da ta Maida ma Ƴan Kasuwa a, Ibadan da Shinkafar su Ƴar Waje da aka kama a cikin Shagunan su a kasuwar.

Majalisar ta bada Umarnin ne a Yau Talata ga Hukumar kwastam da ta maida ma Ƴan Kasuwar Shinkafar su Ƴar Waje da Jami’an Hukumar suka kwace a kasuwar Ojo Oba dake Ibadan, jihar Oyo hakan ya biyo bayan wani samame da Jami’an Hukumar suka kai a kasuwar ranar Asabar din da ta gabata Inda suka kwashe Shinkafar Kimanin tirela Takwas dauke da Buhunnan Shinkafa.

Kazalika Jami’an Hukumar sun gudanar da wani aiki makamancin hakan a cikin watan Mayu a Kasuwar Bodija duk a cikin garin na Ibadan Inda suka tafi da wasu Buhunnan Shinkafa.

Da yake tabbatar da kama Shinkafar, Theophilus Duniya, Mai Magana da yawun Hukumar na federal operation unit (FOU), zone A, yace Doka ta baiwa jami’an Hukumar damar su fasa ko balla Shagunan da suke zargin akwai kayan da aka hana shigowa dasu ƙasar nan.

Kola Balogun, shine Sanata mai wakiltar Oyo ta kudu shine ya gabatar da wannan koken a gaban Zauren Majalisar a maimakon Ƴan Kasuwar.

Daga nan Shugaban Majalisar Sanata, Ahmed Lawan, ya miƙa koken ga Kwamitin dake kula da koke koken Al-umma domin suyi Bincike akan wannan Lamarin na fasa Shagunan Ƴan Kasuwar da Hukumar kwastam tayi a kasuwar Bodija.

Membobin Kwamitin sun nuna bacin ransu akan lamarin sun kumayi Allah wadai da abunda Hukumar ta kwastam tayi inda suka ce ya sa’bama dokar Hukumar ta Shekarar Dubu Biyu da Bakwai wadda Shugaba Olusegun Obasanjo 2007.

Majalisar ta bayyana cewa doka ta baiwa jami’an Hukumar damar su kama kayane da aka shigo dasu ta haramtacciyar hanya Kilometer Arba’in da Iyakokin Najeriya.

Kwamitin ya Buƙaci Hameed Ali, ƙwanturola Janar na kwastam, da ya tabbatar da cewa kayan da aka kama an maidasu zuwa ga Ƴan Kasuwar cikin Makonni Biyu.

An kuma Umarci Hukumar da ta Bud’e ma Ƴan Kasuwar Shagunan su da aka Garƙame, kudaden da kuma ake zargin an kwashe yayin aikin a maidoma Ƴan Kasuwar kayansu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here