Advert
Home Sashen Hausa An Soma Gudanar Da Taron Makon Hadin Kan Musulmi Na Shekara-shekara A...

An Soma Gudanar Da Taron Makon Hadin Kan Musulmi Na Shekara-shekara A Katsina

Sheikh Yaqub Yahaya a wajen taron makon hadin kan Musulmi

Daga A.I Musa.

Kamar kowace shekarara, bana ma, ‘yan’uwa almajiran Sayyeed Ibraheem Yaqoub Zakzaky(H) na da’irar Katsina, sun soma gabatar da taron makon hadin kan al’ummar Musulmi.

Taron Makon hadin kan Musulmin na bana wanda ake gudanar da shi Unguwar filin Fayis da ke cikin birnin na Katsina, an shiga rana ta biyu ta gudanar da shi.

An dai fara taron ne da baje kolin mawaka a ranar farko a jiya Alhamis, ranar da ake kira da “daren mawaka.”

A daren yau juma’a da aka shiga rana ta biyu a taron, Shaikh Injiniya Muhammad Lawal daga gidan darikar kadiriyya na Katsina ne ke gabatar da jawabi a taron mai taken ‘Muhimmancin Raya Tarukan Maulidin Manzon Allah(S).’

Wani bangare na Mahalarta Taron

Tuni dai shehin malami ya soma jawabin maudu’insa inda yake amfani da wani irin salon jawabi wajen isar da sakon da mau’in nasa yake kumshe da shi ga dimbin jama’ar da suka yi tururuwar sauraron sa.

Wakilin ‘yan’uwa musulmi na Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ne mai masaukin baki kuma mai gabatar da ta’alikin jawabi a taron.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...