Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa, NAFDAC ta gargaɗi ƴan Nijeriya cewa, akwai wasu kayan abinci da a ka shigo da su cikin ƙasar.

Kayaiyakin abincin, in ji NAFDAC, sun haɗa da Continental Mills da Great Value Buttermilk Pancake da Waffle Mix, inda ta ce ta na gargadin ne sabo da yiwuwar gurbacewar kayan daga kasashen waje.

Sanarwar da Darakta-Janar na NAFDAC, Moji Adeyeye ya fitar a jiya Lahadi ta ce, an rarraba kayan a duk fadin kasar a Amurka, inda masu sayen kayayyakin suka sayi kayan daga shagunan sayar da kayayyaki na Walmart.

Hukumar ta buƙaci masu shigo da kaya, masu rarrabawa, dillalai, masu samar da lafiya, da masu amfani da su da su yi taka-tsan-tsan wajen shigo da kayayyaki, rarrabawa, siyarwa, da amfani da samfurin da aka dawo dasu.

Hukumar ta NAFDAC ta yi kira ga jama’a da suka mallaki wannan samfurin da su daina sayarwa ko amfani da su tare da mika haja ga ofishin NAFDAC mafi kusa.

“NAFDAC tana ƙarfafa ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya, masu siye da marasa lafiya da su ba da rahoton munanan abubuwan da suka shafi amfani da wannan samfurin zuwa ofishin NAFDAC mafi kusa, NAFDAC PRASCOR ko a kirawo 20543,” in ji sanarwar NAFDAC.

“Jama’a na iya ba da rahoton duk wani mummunan tasiri ta pharmacovigilance@nafdac.gov.ng ko ta NAFDAC ADR e-Reporting dandali da ke www.nafdac.gov.ng,”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here