Advert
Home Sashen Hausa An sanya ranar buɗe layukan sadarwa a Jihar Zamfara

An sanya ranar buɗe layukan sadarwa a Jihar Zamfara

Da Ɗumi-Ɗumi: An sanya ranar buɗe layukan sadarwa a Jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da shirin buɗe hanyoyin sadarwar kafin ƙarshen wannan makon.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Zamfara, Honorabul Ibrahim Dosara ne ya bayyana haka, yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Zamfara a ranar Alhamis 30 ga Satumba, 2021.

“Gwamnati na tunanin buɗe layukan sadarwar a babban birnin jihar a wannan makon,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar Zamfara ba ta ji daɗin irin halin matsi da jama’ar ta suka shi ga ba ta dalilin katse hanyoyin sadarwa, yana mai jaddada cewa an ɗauki matakin ne da kyakyawar manufa.

Ya yi bayanin cewa ganin hakan, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammad Bello Matawalle ta samar da kayan jin kai ga jama’ar jihar.

“Wata nasarar da muka samu ita ce goyon bayan da muka samu daga mutanen jihar Zamfara.

“Jama’a sun bada goyi baya kuma sun yi addu’a ga gwamnati ta samu nasara.

“Dangane da hakan, Gwamnati ta yanke shawarar raba kayan tallafi na masarufi ga mutane,” in ji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: