An sanya dokar hana fita a garin Jangebe na Zamfara

BBC

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita a garin Jangebe domin kwantar da tarzomar da ta tashi a jiya lokacin mika ‘yan matan sakandiren da aka sace ga iyayensu.

Haka kuma ta sanar da rufe babbar kasuwar garin domin dakile hanyar da masu satar mutane ke fakewa da ita.

“Biyo bayan rikicin da mutane suka tayar a Jangebe bayan dawo da wadannan ‘yan makaranta, gwamnatin Zamfara ta amince ta sanya dokar hana fita a garin,” in ji kwamishinan yada labarai Sulaiman Anka.

Dokar ta fara aiki ne tun a ranar Laraba.

“An sanya dokar ne domin kar a kara samun ta da zaune tsaye,” in ji kwamishinan.

A jiya ne rahotanni suka ambato cewa an samu hatsaniya a garin Jangebe lokacin da gwamnatin jihar ke mika ƴan matan da aka sako ga iyayensu.

Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa hatsaniyar ta faru ne bayan da wasu mutanen garin na Jangebe suka kama jifar sojoji bayan jami’an gwamnati da suka yi rakiyar ɗaliban sun miƙa su ga iyayensu.

“Sojoji sun yi harbi bayan da mutane suka kama jifansu,” in ji wani mazauni garin Jangebe.

Sai dai kwamishinan tsaro na jihar Abubakar Dauran ya ce lafiya lau suka miƙa ɗaliban ga iyayensu, ba ya da masaniya da abin da ya biyo baya.

Abdulmalik Saidu Maibiredi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here