An samu sa’bani tsakanin NNPC da PPPRA…

Ma’aikatar Samar da Man Fetur ta ƙasar Najeriya wato NNPC ta Musanta ƙarin Kudin Man Fetur Inda ta bayyana cewa har yanzu farashin Man yanan yadda yake baayi ƙari a wannan watan na Maris ba.

Hakan ya sa’ba da wata sanarwa da Ma’aikatar Kula da sanya Daidaito a farashin Man Fetur din wato PPPRA ta fitar wadda kawo yanzu Ma’aikatar da goge Sanarwar kamar yadda shafinsu ya nusar.

Tunda farki dai ita Ma’aikatar ce ta fitar da Alƙalumma da suke nuna yiyuwar karin kudin saida Man Fetur din tundaga Depo zuwa ga Yan kasuwa, wanda hakan yasanya ake cigaba da samun dogayen Layuka a Gidajen Man Fetur a fadin ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here