An Samu Mahaukaciya da Bindigu a Lagos..

By Muhammad Aminu Kabir

Abun mamaki baya ƙarewa a duniya, an kama wata mata da sunan Mahaukaciya a jihar Lagos a Unguwar Abule- Ado a yankin da ake kasuwar Duniya wato Trade fair Badagry.

Abun Mamakin shine an samu wannan Mahaukaciya da Bindigu ƙirar Ak 47 har Guda Ukku da kuma wasu sassan jikin Ɗan Adam, Jama’a basuyi wata wata ba Inda suka banka mata wuta ta ƙone ƙurmus.

Bisa ga zargin da jama’a keyi shine Matar tana ɓoye Bindigun ne domin masu fashi da makami dake yankin kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani daga Jami’ai dangane da Afkuwar Lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here