An sako ƙarin ɗaliban makarantar Bethel Baptist 10 daga hannun ƴan bindiga

An sako ƙarin ɗalibai goma na makarantar sakandire ta Bethel Baptist High School ta Kaduna daga hannun ƴan bindiga.

Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Joseph Hayab ya tabbatar wa BBC cewa an sako ɗaliban ne ranar Lahadi kuma kawo yanzu akwai sauran ɗalibai 11 a hannun ƴan bindigar.

A makon da ya gabata ne ran 18 ga watan Satumba ƴan bindigar suka sako wasu ɗaliban 10 bayan sama da kwanaki 70 a hannunsu.

Mista Hayab ya ce tuni aka miƙa ɗaliban ga iyayensu.

 

A watan Yuli ne wasu ƴan bindiga suka shiga makarantar ta Bethel Baptist High School a jihar Kaduna kuma suka yi awon gaba da ɗalibai sama da 100.

Tun daga lokacin, ƴan bindigar sun riƙa sako ɗaliban bi da bi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here