Advert
Home Sashen Hausa An sakar wa marubuci Shehu Gombe mara bayan sasantawa

An sakar wa marubuci Shehu Gombe mara bayan sasantawa

An sakar wa marubuci Shehu Gombe mara bayan sasantawa

MARUBUCIN nan wanda aka zarge shi da sace kuɗin ladar cin gasar rubutun adabi a Katsina ya samu ‘yancin sa bayan ya kwana biyu a sel ɗin ‘yansanda.

Hakan ya biyo bayan sasantawar da aka yi tsakanin marubucin, Malam Shehu T. Abdullahi Gombe, da wanda ya zo na ɗaya a gasar, Malam Bishir Adam.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa wasu daga cikin ‘yan kwamitin shirya gasar ne su ka sasanta marubutan biyu a ofishin ‘yansanda na GRA da ke birnin na Dikko.

Sasantawar ta yiwu ne bayan da mahaifiyar Bishir ta shigo cikin al’amarin, inda ta buƙaci ɗan ta da ya yafe ya janye ƙarar daga wurin ‘yansanda.

Majiyar ta ce wasu ‘yan’uwan Bishir ne su ka tsaya kai da fata a kan lallai sai an ci gaba da tuhumar Shehu har zuwa kotu, amma shi zakaran gasar bai lamunta da hakan ba.

“Tun da fari, Bishir ba ya so ya haɗa Malam Shehu da ‘yansanda amma waɗannan ‘yan’uwan nasa su ne su ka iza shi,” inji mai ba mu labarin, wanda ya ce a sakaya sunan sa.

Bayan an sake shi, Shehu tare da su fitaccen marubuci kuma jarumin finafinai Ado Ahmad Gidan Dabino sun je gidan marubuciya Hajiya Aisha Mobil inda su ka ci abinci.

Da ma tun da safe sai da Aisha Mobil, wadda ita ce ta fara lashe gasar rubutun mata ta ‘Hikaya Ta’ da BBC Hausa ke ɗaukar nauyi a duk shekara, ta kai wa Shehu abinci a ofishin ‘yansandan ita da wasu mutum biyu.

A wajen ‘yansandan sai da aka sanya ta ta ɗanɗana abincin da ruwan shan kafin a bari Shehu ya ci, kamar yadda dokar ‘yansanda ta ke.

Daga baya, Mobil da Fatima S. Mohammed su ka koma gidan Mobil bayan sun yi jiran zaman isowar mai ƙarar da mahaifiyar sa.

Bayan awa uku aka kira su aka ce an sasanta, kuma ga su Shehun nan za su je gidan ta domin su kimtsa.

Da su ka isa gidan, Mobil ta shirya masu tuwo su ka ci.

Majiyar ta ce Shehu, wanda Bafillacen Gombe ne, ya ci gaba da kasancewa cikin damuwa, har ma ya kasa cin abincin sosai, sai ma ya buƙaci a ba shi fura idan akwai.

Da ya ji an ce babu nono sai yogot da za a dama masa furar da ita, sai ya ce a bar ta kawai.

Haka kuma an tambaye shi idan ya na so ya ɗan watsa ruwa, amma ya ce a’a a bari ya gode.

Daga baya, bayan sun ɗau hotuna, sai Gidan Dabino ya ɗauke shi zuwa Kano, inda zai kwana kafin ya tafi gida Gombe a gobe.

Wata majiyar tamu ta daban ta ce marubuta sun yi wa Shehu karo-karo na kimanin N85,000, amma babu tabbacin an ba shi kuɗin kafin ya tafi.

Daga hagu a tsaye, Shehu Gombe, Fati, Ado Gidan Dabino da Aisha Mobil bayan cin abinci a gidan Mobil
Shehu T. Abdullahi Gombe a ofishin ‘yansanda na GRA a Katsina … kafin a sasanta

Majiyar ta ce ana sa ran cewa kuɗin za su ƙaru nan da gobe, sannan a haɗa a ba shi.

Idan kun tuna, an sace wa Bishir Adam kuɗi N250,000 na ladar sa ta lashe gasar “Rubutun Labaran Hausa a kan Muhalli” wadda wani babban ɗan siyasa a Katsina, Architect Ahmed Musa Ɗangiwa, ya ɗauki nauyin shiryawa.

Ɗangiwa shi ne Manajan Darakta na Bankin Lamunin Mallakar Gida na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria, FMBN).

An sace kuɗin Bishir ne jim kaɗan bayan an tashi daga taron bada kyaututtuka ga zakarun da su ka yi nasara a gasar, kuma Gwamna Aminu Bello Masari ya na daga cikin manyan baƙi da su ka halarta.

Bishir ya zargi Shehu ne domin ya ba shi jakar da kuɗin ke ciki ya aje masa lokacin da za su ɗau hoto amma da ya karɓi jakar daga baya sai ya ga an zare ambulan ɗin da kuɗin ke ciki.

Shehu ya musanta zargin a hirar da ya yi da mujallar Fim a daren shekaranjiya, jim kaɗan kafin a kama shi.

A cewar sa, haƙiƙa Bishir ya ba shi ajiyar jakar, amma daga baya ya zo ya karɓi abar sa, kuma sai bayan wani lokaci ya kira shi ya faɗa masa cewar an fa sace masa kuɗin ladar lashe gasar.

Yunƙurin da masu shirya gasar su ka yi don su kashe maganar tun a shekaranjiya ya ci tura, wanda ya sa aka kama Shehu har ya kwana a sel, ya wuni a hannun ‘yansanda, kuma ya ƙara kwana, sannan ya yi rabin wuni.

Yawancin marubuta sun tausaya wa Shehu kan ƙaddarar da ta auka masa.

Waɗanda su ka san shi sun yi masa kyakkyawar shaida, su ka ce ko kaɗan ba zai aikata irin wannan mugun abu ba.

Shi ma Bishir an tausaya masa kan asarar da ya yi, ana cewa ya ga samu ya ga rashi.

Wasu marubutan sun yi nuni da cewa mai yiwuwa ne wani daga cikin ‘yan daba tare da jagaliyar siyasa da su ka cika wajen taron ne ya faki idon mutane ya zare wa Bishir kuɗin.

Da yawa sun yi addu’ar Allah ya tona asirin wanda ya tafka wannan aika-aika tare da bi wa kowa haƙƙin sa.

Munciro wan’nan labarilabarin ne daga mujallar Film magazine. Dake busa yanar gizo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

BOKO HARAM TA KUSA ZUWA TARIHI …Inji BULAMA BUKARTI

Muazu hassan @Jaridar Taskar Babarai Daya daga cikin masana akan yan kungiyar boko haram Barista Bulama Bukarti ya rubuta cewa ga dukkan alamu boko haram...

ANA SIYAR DA FOM …A silicon Height International College

@Katsina City News Hukumar Makarantar Height International College tana ci gaba da siyar da fom na shiga ajujuwan Reno (Nursery) da Firamare da kuma Sakandare. Makarantar,...

Dauke Layukan Sadarwa: Khalifan Tijjaniya Ya Yi Kira Ga Gwamna Masari..

Dauke Layukan Sadarwa: Khalifan Tijjaniya Ya Yi Kira Ga Gwamna Masari... Daga Hussaini Yero Madogara TV/Radio Sakamakon mawuyacin hali da al'ummar yankunan da aka dauke layukan...

PHOTO NEWS: Arc Kabir Ibrahim FNIA elevated to the class of Fellows of the Nigerian institute of architects

Arc Kabir Ibrahim FNIA elevated to the class of Fellows of the Nigerian institute of architects; On Wednesday 20/10/2021 at international conference centre Abuja and...
%d bloggers like this: